Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya ce zai zama abin kunya idan ya ambaci sunan takwaransa na jam’iyyar Labour Party (LP), Peter Obi. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Tinubu ya bayyana haka ne a yayin da yake jawabi a wani gangami a Gbaramatu na, jihar Delta a ranar Juma’a.
KARANTA WANNAN LABARIN: Nasarawa: PDP Ta Sake Sanya Ranar Yakin Neman Zaben Ta Bisa Bin Umarnin ‘Yan Sanda
A cewar tsohon gwamnan Legas, “kididdigar kuskure” daga Obi ba shine abin da Najeriya ke bukata a halin yanzu ba.
Tinubu ya ci gaba da bayyana kansa a matsayin daya daga cikin ‘yan takarar shugaban kasa da har yanzu ke kan gaba.
Ya ce: “Sa’ad da na tsaya a gabanku, akwai kaɗan daga cikinmu da suka rage a masu neman. Wani yace Atiku ne. Sau nawa yake nema? Koyaushe yana ta nema ya gaji. Ka ce masa ya je ya huta, Ya isa ya isa.
“Wani kuma na tunanin da kididdigar shi zamu fadi. Ya kwanta da lissafin da babu wani Ba’indiye da zai iya warwarewa. In ambaci sunansa abin kunya ne a gare ni. Ba zan ambaci sunan shi ba. Ƙididdigar ba gaskiya bane , – wannan ba shine abin da Najeriya ke buƙata ba.” Inji shi.
A wani labari kuma, ‘Yan Sanda Sun Cafke Wasu Dalibai Mata Guda Biyu Bisa Laifin Cin Zarafin Wata Malama
Rundunar ‘yan sandan jihar Edo ta cafke wasu dalibai mata biyu na makarantar sakandaren Adesuwa da ke Benin bisa zargin cin zarafin wata malamar su.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, SP Chidi Nwabuzor, ya tabbatar da kamen a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a a garin Benin.