Ministan Sufuri na tarayya, Engr Mu’azu Sambo ya yaba da kokarin gwamnatin Muhammadu Buhari, inda ya sanya ta a matsayin wadda tayi nasara.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa Ministan ya ce tun bayan samun ‘yancin kan kasar, bata taɓa dace da shugaba irin Buhari ba, wajen zuba jari don bunkasa ababen more rayuwa a Najeriya.
Ministan na wannan magana ne a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai, bayan ya duba tashar Mobolaji Johnson Mega na layin dogo na Lagos-Ibadan.
Gwamnatin Buhari ta Amince da Samar da Sabbin Jami’o’i Masu Zaman Kansu 33
Sambo ya samu rakiyar babbar daraktar hukumar kula da zirga-zirgar jiragen kasa ta Najeriya Engr Fidet Okhiria, da sauran jami’an gudanarwa na layin dogo, da babbar sakatariyar ma’aikatar sufuri Dr. Magdalene Shani, da kuma manajan daraktoci na sauran hukumomin gwamnati masu alaka a ma’aikatar sufuri.
Ya ce ba tare da nuna rashin son kai ba, ko a matsayinsa na cikin gwamnati, yana alfahari da cewa gwamnatin Buhari ita ce ke kan gaba a duk sauran gwamnatocin da suke da niyyar samar da ababen more rayuwa.
A cewarsa, don jaddada kudirin gwamnati na samar da ababen more rayuwa, gwamnatin Buhari ba kawai ta samar da shirin raya kasa na 2021-2025 ba, tana kuma da abin da ta kira shirin bunkasa ababen more rayuwa na fadar shugaban kasa, wanda da shi ke tafiyar da wasu muhimman ayyuka daya gada.
Ya ce gwamnati za ta ci gaba da da yin duk mai yiwuwa, wajen ci gaba tare da jajircewar wajen samar da ababen more rayuwa.
A kan komawar jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna, Sambo ya ce zai zama rashin nuna kulawa, idan aka dawo da aikin jirgin kasa a kan hanya mai matukar muhimmanci ba tare da Gwamnatin Tarayya ta kubutar da dukkan wadanda ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da su ba a ranar 28 ga Maris, 2022 ba.