Ɗan Wasan Tsakiyan Najeriya Wilfred Ndidi ya gargaɗi ƴan wasan ƙwallon ƙafa na Super Eagles dasu yi taka tsantsan da wasan samun tikitin shiga gasar wasan ƙwallon ƙafa ta Duniya na Shekarar 2022, tsakanin Najeriya da Ghana.
Ya bada wannan gargaɗin a zantawar sa da Kamfanin Dillancin Labaru na ESPN.
Najeriya dai zata Fafata da Ghana a filin wasa na Cape Coast Sports Mai cin mutane dubu 20,000 daga ƙarfe 7: 30 na safen ranar Juma’a 25 ga watan Maris, da kuma sake wani a filin wasa na Moshood Abiola daw Abuja a ranar Talata 29 ga watan Maris daga ƙare 6 na dare.
KARANTA WANNAN LABARIN: 2023: Bayan Nayi Shekaru 8 ina Mulki, zan miƙa ma Ɗan siyasar daya fi kowa Masoya — Cewar Tinubu
Duk wanda yaci wasan, zai samu tikitai guda biyar ga gasar wasan ƙwallon ƙafan karo ta w2, da zai fara a ranar 14 ga watan Nuwamba zuwa 18 ga watan Disamba na wannan shekarar a Ƙasar Qatar.
Yace “zamu samu dama sosai idan muka samu tikitin shiga wasan ƙwallon ƙafan na Duniya.
“Ammafa Ghana bata da sauƙi. A gaskiya, dole sai mun zama masu taka tsantsan akan Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa tasu, bawai ga wani ɗan wasa ba. Zai zamanto wasa mai wahala.”
Haka zalika, Kocin Kungiyar Augustine Eguavoen yayi kira ga Captain Ahmed Musa, da Mataimakin sa Captain William Ekong, da Ɗan wasan tsakiya Ndidi, dana gaba Moses Simon da Kelechi Iheanacho a cikin sunayen da zasu wakilci Najeriya a Gasar wasan ƙwallon ƙafa na Duniya a Qatar da sauran su.