Shugaban kasa, Muhammadu Buhari da takwaransa na kasar Poland, Andrzej Duda, sun rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna kan harkokin noma domin karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu a fannin.
Duda ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a kofar dakin taro na fadar shugaban kasa, dake Abuja jim kadan bayan ganawar sirri da Buhari.
A cewarsa, yarjejeniyar ta zama dole bisa la’akari da cin zalin Rasha akan Ukraine da kuma matsalar karancin abinci.
Da yake kwatanta cin zarafin Rasha Mr Duda ya lura cewa kasarsa tana tallafawa jihohin da abin ya shafa da kuma kasashen da ke kawance da su don bunkasa yawan amfanin gona.
KARANTA ANAN: Yajin Aikin ASUU: Ministan Ilimi Ya Shiga Ganawar Gaggawa Da Shugabannin Jami’o’i
A fannin makamashi, ya yi nuni da cewa, Nijeriya, kasancewar tana da arzikin iskar gas, za ta tabbatar da ci gaba da samar da iskar gas ga kasar Poland da ma sauran kasashen Turai.
A nasa bangaren, Buhari ya mika godiyarsa ga gwamnatin Poland bisa bude wa daliban Najeriya da rikicin Rasha da Ukraine ya daidaita wani fage na ci gaba da karatunsu; don samun damar ci gaba da ilimi.
Ya yi nuni da cewa, kasashen biyu sun cimma yarjejeniyoyin kara hadin gwiwa a fannin noma, makamashi da tsaro.
Bayan kammala jawabin Buhari da shugaban Poland din sun zarce zuwa dakin taro na Banquet dake fadar gwamnatin tarayya domin cin abincin rana.
A wani labarin kuma: Rikicin PDP: Wike ya yi barazanar yi wa makiyansa bulala a 2023
Yayin da rikicin cikin gida na babbar jam’iyyar adawa ta PDP ke ci gaba da yin ƙamari Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya ce zai yi wa makiyan sa na siyasa bulala mai ‘bakono’ a zaben 2023 mai zuwa.
Ya ce ba zai taba barin wani abu ga Allah ba.
Wike ya bayyana hakan ne a matsayin martani ga shawarar da Gwamna Okezie Ikpeazu ya ba shi na ya bar duk wasu kura-kurai da ake yi masa na siyasa don Allah a lokacin da yake gudanar da wani aiki a jihar a Umuahia, babban birnin jihar Abia.