Kusan watanni uku bayan rufe kan iyakokinta na kan tudu da ta yi, gwamnatin Nijeriya ta sanar da kwace haramtattun kayayyakin da darajarsu ta kai naira triliyan 2 da biliyan 300, wadanda aka yi yunkurin fasakaurin shigar da su cikin kasar.
Kakakin hadin gwiwar jami’an tsaron dake aikin Sintirin kan iyakokin Nijeriyar na kan tudu, Joseph Attah ya ce kayayyakin da suka yi nasarar kwacewa sun hada da bindigogi, alburusai, ababen hawa, magunguna, shinkafa, da kuma tankunan man fetur.
Attah ya kuma ce, jami’an tsaron hadin gwiwar da suka hada da na Kwastam, shige dafice, ‘yan sanda da sojoji, sun kame bakin-haure 203 dake kokarin satar shiga Najeriya, sai kuma masu safarar mutane guda 8.
Ranar
20 ga watan Agustan da ya gabata, shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bada umurnin
rufe iyakokin kasar na kan tudu, na wucin gadi, domin kawo karshen matsalar
fasakaurin haramtattun kayayyaki cikin kasar, daga kasashe makwabta.