Mataimakiyar shugaban kasar Amurka, Kamala Harris ta karbi bakuncin takwaranta na Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo a fadar White House dake birnin Washington DC.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Kasashen biyu sun gana ne domin tattauna alakar Najeriya da Amurka da kuma shirin mika wutar lantarki a Najeriya, a cewar sanarwar daga sassan biyu.
“Hakika abin farin ciki ne na gana da mataimakiyar shugaban kasa Kamala Harris don tattaunawa kan shirin #EnergyTransition na Najeriya da sauran muradu tsakanin gwamnatocin mu,” in ji Osinbajo a cikin wata sanarwa.
“Amurka ta kasance abokiyar zamanmu da dadewa kuma tun daga plokacin da muka samu ‘yancin kai, tana goyon bayan burin Najeriya na ci gaban tattalin arziki da zamantakewa.
Karanta kuma: Osinbajo Ya Gabatar Da Wata Yarjejeniyar Musayar Bashi Da Sauyin Yanayi A Amurka
“Bugu da ƙari, sadaukar da kai ga dimokraɗiyya, dole ne kasashen biyu su ci gaba da yin aiki tare a matakan ɓangarorin biyu da na bangarori daban-daban don magance ƙalubale bai ɗaya a duniya, da nufin inganta zaman lafiya da tsaro, da magance annoba, sauyin yanayi, da kuma matsalolin tattalin arziki.”
Gidan talabijin na channels ya rawaito, Harris ta bayyana jin dadin ta da ganawa da mataimakin shugaban kasa Osinbajo.
“Ya yi matukar kyau da muka gana da mataimakin shugaban Najeriya Osinbajo a yau domin tattaunawa kan karfafa dangantakar dake tsakanin Amurka da Najeriya,” in ji ta.
“Shugabancin Afirka, musamman, shugabancin Najeriya, shi ne mabuɗin tinkarar kalubalen yanki da na duniya.”
A wani labarin kuma: Ku Cire Siyasar Kabilanci Da Addini, Jonathan Ya Shawarci Matasa
Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya bukaci matasa da su yi watsi da masu kokarin raba kasar da siyasar kabilanci da addini gabanin zaben 2023.
Gidan talabijin na channels ya rawaito cewa, Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a Owerri a wajen taron cika shekaru 80 na Cif Emmanuel Iwuanyanwu.