Nijeriya na buƙatar 100,000MW domin magance matsalar wutar lantarki — Tsohon Minista
Tsohon Ministan Wutar Lantarki, Farfesa Barth Nnaji, ya baiyana cewa Nijeriya na buƙatar megawat dubu 100 na wuta in har ta na buƙatar magance matsalar wutar lantarki a ƙasar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kotu ta bada belin Muhuyi Rimingado
Nnaji ya baiyana hakan ne a yayin ganawa da manema labarai a kan makomar wutar lantarki a ƙasa a yau Juma’a a Enugu.
Ya ce ƙasar na fama da matsaloli wajen samar wa, yaɗa wa da rarraba wutar lantarki s ƙasa.
Ya ce duk wannan shi ne ya sanya zai yi wuya a samu isashshiyar wutar lantarki ga ƴan kasa.
Comments 1