Tsohon shugaban kasar Najeriya Olusegun Obasanjo ya ce kasar yanzu haka rana buƙatar shugaba mai kishin son ci gaba, da kuma tabin hankali wajen gyaruwar ta.
Obasanjo ya bayyana hakan ne yayin da ya karbi Bakuncin guda cikin yan takarar shugaban kasa, a jam’iyyar PDP Mohammed Hayatudeen, wanda ya kaima masa ziyara a gidansa dake Abeokuta.
Ya kara da cewa yanzu haka shi yana da irin tabin hankalin da Najeriya ke bukata, kuma baya nadama kan samun kansa cikin wannan yanayi.
Ya kuma yanayin da Najeriya ke ciki yanzu haka abin damuwa ne matuka gare shi, dama duk wani mai kishin son ci gaban ta.
Da yake tabo bangaren tsaro kuwa, Obasanjo ya ce Duk da kalubalen da bangaren ke fuskanta, cikin shekaru biyu za a iya magance shi, matsawar aka samu shugaban da ya dace.
Da yake jawabinsa tunda fari, Mohammed Hayatudeen yace Najeriya nan gaba kadan zata zama abar kwatance ta fuskar ci gaba matsawar aka samu wanda ya san me yake, kuma aka bashi mulkin ta.