Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta kuma dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar PDP, ya ce Najeriya na matukar bukatar shugabannin da za su rika ganin sassan kasar nan a matsayin kasa daya dunkulalliya.
Okowa ya bayyana haka ne a ranar Litinin a lokacin da ya karbi bakuncin Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, da Mai Martaba Dokta Benjamin Ikenchukwu, Keagborekuzi I, Dein na Agbor a Gidan Gwamnati, Asaba.
KARANTA ANAN: FG ta roki ma’aikatan jinya da su zauna a Najeriya
Ya ce al’ummar Najeriya na matukar bukatar shugabanni da za su ga irin karfin da ke tattare da bambancin al’umma da samar da Masalaha, maimakon amfani da shi wajen raba kasar.
Ya ce ziyarar da Sarkin Kano ya kai jihar Delta, wata alaka ce da za ta taimaka wajen hada kan al’umma da samar da zaman lafiya, don haka ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su rika kallon kan su a matsayin ‘yan uwan juna, ba tare da la’akari da bambancin ra’ayi ba.
Ya yi kira da a yi amfani da gogewa da hikimar sarakunan gargajiya a kasar nan ta hanyar samar musu da mukamai na doka bisa la’akari da irin gudunmawar da suke bayarwa wajen ci gaban al’umma.
Okowa ya ce akwai bukatar a bai wa Iyayen kasa masu sarauta manyan ayyuka a harkokin mulkin Najeriya saboda sun taka muhimmiyar rawa wajen ganin an hada kan jama’a.
Tun da farko, a nasa jawabin, Sarkin Kano Ado Bayero, ya ce ya kai ziyarar ne domin tabbatar da dadewar alaqa tsakanin Kano da jihar Delta.
Bayero ya ce tattaunawar rashin hadin kan al’umma yau abu ne da ‘yan Najeriya za su zauna su tattauna domin a baya an yi ta cikin nasara.
Ya kuma yi imanin cewa a matsayin hukuma, ba za a iya zargi gwamnati da komai ba saboda kowa yana da rawar da zai taka.
Ya ce idan aka yi shugabanci na gari al’amura za su daidaita ga kasa.
A wani labarin kuma: Hukumar Civil Defence ta kamata litar mai adadi mai yawa da aka sace
Jami’an tsaron Najeriya da jami’an tsaron farin kaya a Kuros Riba, sun cafke lita 16,000 na albarkatun man fetur da aka sace a jihar.
Kwamandan NSCDC na jihar, Mista Samuel Fadeyi, ya ce kayayyakin da aka sace wadanda akasarinsu gas ne, amma an ajiye su ne a cikin ganguna da galan kuma an boye su a wuraren shakatawa na tirela a fadin jihar.