Sakataren zartarwa na cibiyar samar da albarkatun Gona ta HEDA, Sulaimon Arigbabu, ya ce Najeriya tana daya daga cikin mafi karancin filin noma.
Arigbabu ya bayyana hakan ne a jiya Talata yayin da yake magana a wajen wani taro mai taken ‘Tsaron Abinci, Gina Jiki, da wadatuwar Abincin’.
Da yake magana a gidan a yayin taron daya gudana ta Allahu n gani gaka Arigbabu ya ce kusan kashi 40 cikin 100 na abincin da ake nomawa a Najeriya na yin barna ne a tsakanin gonaki da masu amfani da su na karshe.
Ya ce, “Kusan kashi 40 cikin 100 na abincin da muke nomawa a Najeriya, ana bata shi ne a tsakanin gonaki da masu amfani da su na karshe amma babu wanda ya yi maganar damar da muka rasa, abincin da ba mu noma ba, wanda ke mutuwa tun kafin azo wajen girbi.
“Najeriya tana da tan 1.2 a kowace hekta kuma a Asiya, tan 4-7; a Masar, tana da tan 10 a kowace hekta.
A fannin masara, Masar tana da tan 6, Afirka ta Kudu tana da tan 5.1, Najeriya tana da tan 1.6.” Ya alakanta karancin kadada da karancin ilimin da manoma ke samu kan aikin gona.
“Saboda karancin ilimin manoman ne ta fannin aikin gona mai kyau, Domin ba ma baiwa manomanmu damar samun ingantacciyar, abin dogaro, da bayanan yanayi na kan lokaci.
“Manoma da yawa suna zuwa wurin manoma ne a lokacin da bai kamata ba, don haka damar da aka rasa shi ne babban dalilin da ya sa muke fama da matsalar karancin abinci, idan muka yi tir da hakan, za mu iya magance asarar bayan girbi.
“Duk da matsin lambar da duniya ke mana, ya kamata Najeriya ta zama cibiyar samar da abinci ga yankin Sahel na yammacin Afirka amma muna rasa wannan damar saboda adadin abincin da ma ba mu iya nomawa ya fi wanda muke nomawa sosai. suna yin asara kuma idan muka dakatar da asarar bayan girbi misali, da kashi 80 cikin 100 za mu kula da wadanda ba za su iya samun abinci mai kyau da gina jiki ba,” inji shi.