- Dole Ne Gwamnati Ta Faɗaɗa Tsarin Gudanarwa
- Mutane Da Dama Na Ƙoƙarin Ɓallewa Daga Ƙasa
- Ba Dole Mu Iya Samun Damar Zagayowar Wannan Rana Ba a matsayin Ƙasa Ɗaya
Farfesa Wole Soyinka, fitaccen marubuci kuma malami a ɓangaren turanci yace ba dole ne Najeriya ta iya kaiwa zuwa wata ranar ta zagayowar murnar ranar ƴancin kai ba muddun shugaba Buhari baiyi ƙoƙarin faɗaɗa tsarin gudanar da gwamnati ba.
Soyinka ya bayyana hakan ne jiya a yayin wata tattaunawa da ƴan jarida dangane da bikin ranar ƴanci ta 12 ga watan Yuni, inda ya bayyana cewa Najeriya kamar jirgi ne da yake gab da rikitowa, saboda haka kowane ɗan ƙasa na da damar ficewa kafin ya kife da shi.
Ya kira yi shugaban ƙasa akan yayi ƙoƙarin tunkarar ƙalubalen da ke fuskantar Najeriya ba wai ya tsaya yana ba na ƴan ƙasa ƙwarin gwuiwar haka nan ba.
Karanta wannan: Hukumar Alhazan Najeriya ta ce za ta mayar wa kowanne Maniyyaci kudinsa

“Hakan shine yasa mutane ke fitowa kan tituna suna zanga-zanga ba tare da jin shakkun jami’an tsaro ko kuma jin tsoron duk wata barazana da za’a yi musu ba. Saboda inda kasa ta kasance tana dab da durkushewa, to lallai dole ne duk waɗanda suke ganin basu cancanci zama a kife dasu ba na da ikon direwa waje.”
Jaridar Guardian ta ruwaito Marubucin na bayyana cewa yawaitar masu son ɓallewa daga ƙasa da ake ƙara samu nada nasaba da ƙin shugaban na sauraron ƙorafe-ƙorafen ƴan Najeriya.
Da aka tambaye shi kan ko yana tunanin Najeriya zata iya cigaba da zama ƙasa ɗaya, sai ya kada baki yace: ” Muddun zata cigaba da tafiya a haka, muddun gwamnati zata ƙi faɗaɗa tsarin gudanar da gwamnati cikin gaggawa, to lallai ba zata iya cigaba da zama a matsayin ƙasa ɗaya ba.”
“Ba wai Wole Soyinka bane ya fara faɗar hakan, mutane da dama sun faɗi hakan. Tsofaffin shuwagabannin ƙasa sun faɗi hakan, ƴan siyasa da dama, masu hasashe da masana tattalin arziƙi duk sun faɗi hakan, mun sha faɗa har munma gaji da faɗi.”
“Lallai ƙasar na ƙan gaɓar rugujewa indai ba’a gyara ba, kuma bani kaɗai bane ke faɗin hakan, muddun gwamnatin Buhari bata yi ƙoƙarin daukar mataki ba, to lallai ba dole mu iya sake riskar zagayowar wannan rana ta samun ƴancin kai a matsayin ƙasa ɗaya ba.”
Da yake magana akan batun dakar da tuwita, Wole Soyinka yace ƙoƙarin daƙile hanyoyin da jama’a zasu iya bayyana ra’ayinsu kamar ƙoƙarin daƙile ainihin samuwar ƴanci ne.