Najeriya na matukar karuwa da Kasar Pakistan, cewar Buhari
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nuna godiyarsa ga Kasar Musulunci ta Pakistan, kan irin taimako da takewa jami’an kasar Najeriya.
Shugaba Buhari ya fadi hakane lokacin da ya karbi bakuncin Jagoran jami’an hadin guiwa na Kasar Pakistan, Gen Nadeem Raza.
KARANTA:-Najeriya da Kasar Gambia za su hada kai wajan kawo karshen ta’adanci
Mai ba shugaban kasa shawara ta fannin kafafen watsa labarai Femi Adesina ya bayyana haka a cikin wani bayaninsa.
Yace ” Kasar Pakistan tana matukar kokari wajan horas da Jami’an Najeriya”
Buhari yace ” Ina farin ciki sosai kan yadda kasar Pakistan ke jajircewa wajan baiwa jami’an mu horo kala-kala, a kwai wasu daga cikin abokan aikina wadanda suka samu horo a kasar, kuma koda bayan haka kunyi kokari sosai da cigaba da ba jami’an mu dabaru da salo iri-iri. Nayi farin ciki sosai ina mai godiya da hakan.”
Nadeem Raza yace “Kasar Najeriya ita ce babbar kawar Pakistan a Afirika, kuma muna girmama tarayyan mu, muna koya kuma muna karuwa da juna.”