Najeriya ta Ƙwato Dubban Makamai a yankin Niger Delta
Cibiyar Kula da Taƙaita Kananan Makamai ta Kasa (NCCSALW) ta kwace bindigogi sama da 3,000 da aka kwato a yankin Neja Delta.
KARANTA WANNAN LABARIN: ASUU ta yi zazzafan martani kan kudirin iyaye na biyan N10,000
Jami’in Cibiyar na kasa Abba Dikko ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da shugaban sashen yada labarai na Rundunar Air Commodore Ewejide Akintunde ya fitar.
Manjo Janar mai ritaya ya bayyana cewa, rundunar ‘Operation Delta Safe (OPDS)’ ta kama makamai daban-daban.
OPDS, wadda ta kunshi dakarun soji, rundunar hadin gwiwa ce da ke aiki a jihohin Kudu-maso-Kudu guda shida.
Jami’an hedkwatar tsaro, da rundunar ‘yan sandan Najeriya, da jami’an tsaron farin kaya da na Civil Defence, da sauran su sun shaida bikin miƙa makaman.
Kwamandan OPDS Rear Adm Aminu Hassan wanda ya wakilci Hedikwatar tsaro ta ƙasa ne ya gabatar da wannan jawabi ga hukumar NCCSALW.
Makaman sun hada da bindigogin AK-47, bindigogin FN, bindigogin Beretta, bindigogin G3, da wasu nau’ikan bindigogi.
Sauran sun hada da Sub-Machine Guns (SMGs), General-Purpose Machine Guns (GPMGs), bindigogin da aka kera na gida, da harsashai iri-iri.
Dikko ya ce cibiyar za ta hada dukkan makaman da aka kwato daga hannun jama’a tare da sarrafa tarin makaman kafin a lalata su.
Hukumar NCCSALW na da hurumin kwato haramtattun makamai kanana da ke hannun hukumomin da ke da alhakin mallakar makamai a Najeriya.