Ofishin kula da basussuka na ƙasa (DMO) shi ne ya tabbatar da alƙaluman a rahotonsa na wucin gadi da ya fitar ranar Laraba.
A cewar rahoton, basussukan da gwamnatin shugaba Buhari ta ciyo ya kai Tiriliyan 18.89.
Kuɗaɗen sun ƙaru ne cikin watanni uku sakamakon bashin Dala biliyan 3.36 da aka ƙara ciyowa daga Asusun ba da Lamuni na Duniya (IMF) domin cike giɓin kasafin kuɗin 2020 da aka yi wa kwasƙwarima, da kuma samar da Naira biliyan 162.557 na shirin Sukuk sai kuma kuɗaɗen da za a biya bashin da masu fiton kaya ke bi.
Har wa yau, ofishin na DMO na hasashen kuɗaɗen za su iya ƙaruwa yayin da za a ƙara ciyo wani a cikin gida da kuma wanda za a ƙara karɓowa daga Bankin Duniya, Bankin Raya Ƙasashen Afirka (AfDB) da kuma Bankin Raya Musulunci domin aiwatar da kasafin 2020.
Idan dai za a iya tunawa sai da Najeriya ta yi wa kasafin 2020 kwasƙwarima ta hanyar rage shi saboda illar da annobar Korona ta yi wa tattalin arziƙi da ma kuɗaɗen shigar da gwamnati ke samu a bana.