Najeriya da sauran kasashen Afirka sun rubutawa kungiyar G20 wasika da su tsawaita musu wa’adin aikin basussuka.
Sun dauki matakin ne don tabbatar da cewa biyan basussuka bai gurgunta tattalin arzikinsu ba.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Rokon na kunshe ne a cikin wata wasika da ministocin kudi na kasashen Ghana, Senegal da Masar suka rubuta a madadin ministocin kudi na kasashen Afirka da gwamnonin babban bankin kasar, kuma aka yi kwafin takardar ga shugabar kungiyar G20, kungiyar tarayyar Afrika AU, Manajan Darakta mai kula da lamuni na kasa da kasa (IMF), shugaban Bankin Duniya.
KARANTA WANNAN: https://dimokuradiyya.com.ng/sheikh-gumi-ya-caccaki-gwamnatin-tarayya-kan-kasa-kawo-%c6%99arshen-ya%c6%99i-da-%c6%b4an-taadda/
A cikin wasikar, Ministocin Kudi na Afirka da gwamnonin Babban Bankin sun ce: “Muna neman tallafin kudi cikin gaggawa daidai da martanin da duniya ke bayarwa yayin bala’in COVID-19 don taimakawa tattalin arzikinmu.
“Karshen shirin dakatar da ba da bashi na G20 (DSSI) a watan Disamba na 2021 yana nufin cewa dole ne kasashe su dawo biyan bashin da ake bin su, duk da tabarbarewar yanayin tatalin arzikin duniya, musamman ga matsakaita da masu karamin karfi a nahiyar Afirka.