Najeriya ta samu sabbin mutane 228 da suka kamu da cutar Covid-19 a Jahohi 13 da Babban Birnin Tarayya Abuja.
Hukumar Kula da Manyan Cututtuka ta Ƙasa ta sanar da kamuwar mutanen a shafin ta a ranar Lahadi, 23 ga watan Janairun shekarar 2022.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wasu Majiyoyi Sun Bayyana Cewa Sojoji Sun Kama Shugaban Kasar Burkina Faso
A cewar Hukumar, yawan mutanen da suka a Jahohin sun haɗa da: Babban birnin Tarayya Abuja nada mutane 110, sai Gombe nada 38, da Lagos nada 32, da Osun nada 14, sai Taraba 12, da Imo nada 5, sai Kaduna nada mutane 5, sai Rivers nada 4, Borno 2, da Kano 2, da Bauchi 1, da Delta 1 gami da Ogun nada 1.
A cewar Hukumar, an sallami mutane 462 bayan sun warke daga cutar.
Haka zalika, a ranar Lahadi babu wanda ya rassu sakamakon cutar, wanda adadin waɗanda suka kamu yakai 3,124.