Najeriya ta samu sabbin mutane 35 da suka kamu da cutar Covid-19 a Jahohi biyar da Babban birnin Tarayya Abuja.
Hukumar Kula da Manyan Cututtuka ta Ƙasa ta sanar da sakamakon kamuwar cutar a bayanan da take fitarwa a kullum a ranar Juma’a 4 ga watan Fabrairu na Shekarar 2022.
Yawan mutanen sun ƙunshi 15 a Jahar Rivers, Katsina 5, Abuja 6, da Gombe 4, da Ekiti 1 sai Kano 1.
KARANTA WANNAN LABARIN: Zazzabin Lassa Ya Kashe Mutane 40, Ma’aikatan Lafiya Hudu Sun Kamu A Watan Janairu – NCDC
Hukumar ta bayyana cewa mutane 89 an sallame su bayan sun warke daga cutar, a yayinda babu ko mutum daya daya mutu.
Hukumar ta bayyana a rahoton ta na ranar Juma’a cewa mutane 67 an sallame su a Abuja a ranar 4 ga watan Fabrairu.
Da sabbin mutanen da suka kamu da cutar, Najeriya ta tabbatar da samun mutane dubu 253,540 a yayinda mutane 229,982 suka warke, sai mutane 3,136 suka mutu a Ƙasar.