Najeriya ta samu sabbin mutane 87 da suka kamu da cutar Covid-19 a Jahohi 10, Abuja
A yayinda aka cigaba da
yaƙi da cutar Covid-19, Najeriya ta samu sabbin mutane 87 da suka kamu da cutar a Jahohi 10 da Babban birnin Tarayya Abuja.
KARANTA WANNAN LABARIN: Shaguna Da Gine-gine Sun Kone Yayin Da Tankar Mai Ta Tada Gobara A Onitsha
Hukumar Kula da Manyan Cututtuka ta Kasa ta sanar da haka a bayanan data fitar a ranar Alhamis 27 ga watan Janairun Sabuwar Shekarar 2022.
A cewar Hukumar, mutanen da suka kamu da cutar sun ƙunshi Lagos da Mutane 25, da Rivers 16, Abuja 15, da Delta 9, da Edo 7, da Gombe 5 da Nasarawa 4, da Kuma Bauchi 3, da Kano da Oyo 1 da kuma Borno 1.
A cewar Hukumar mutane 267 an samu sallame su, sakamakon warkewa da suka yi daga cutar.
Babu wanda ya mutu a dalilin cutar a ranar Alhamis, wanda ya sanya mutane 3,134 suka kamu da cutar.
NCDC tace mutane 9 da 7 da aka samu daga Delta da Edo an same su ne ranar 26 ga watan Janairu.
A halin yanzu an tabbatar da mutane 252,840 waɗanda suka kamu da cutar, a yayinda mutane 228,404 suka warke daga cutar.