Daga: Abbas Yakubu Yaura
Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Cif Femi Fani-Kayode, ya mayar da martani game da kashe shugaban Al-Qaeda, Ayman al-Zawahiri, da wani hari da jiragen yakin Amurka suka kai.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Talata, Fani-Kayode ya yaba wa Amurka bisa kashe shugabannin yakin ‘yan ta’adda kamar Osama Bin Ladin, AbuBakr Al Baghdadi da Ayman Al Zawahiri.
DUBA WANNAN LABARIN: 2023: Tinubu Zai Yi Adalci, Ga Dukkan ‘Yan Najeriya – Shettima
Sai dai ya yi zargin cewa sarakunan ta’addanci a Najeriya suna samun lada maimakon a kashe su.
Ya ce ana rokon ‘yan ta’adda, ana biyansu, ana faranta musu rai, ana ba su lada, har ma ana ba su mukaman sarauta a Najeriya.
“Amurkawa sun kashe Osama Bin Ladin, AbuBakar Al Baghdadi da kuma Ayman Al Zawahiri. Godiya! A Najeriya ba ma kashe ‘yan ta’adda: muna rokonsu, mu biya su, mu gamsar da su, mu ba su lada, mu yi musu ruku’u, mu ba su mukaman sarauta, mu bar su su shiga gidan yari don su ‘yantar da ‘yan uwansu,” ya wallafa a shafinsa na Twitter.
Tun da farko dai rahotanni sun bayyana cewa, an kashe Al-Zawahiri a Afganistan sakamakon wani harin da jiragen yakin Amurka suka kai.
An nada shi shugaban kungiyar ta’addanci bayan mutuwar magabacinsa, Osama Bin Laden.
A Wani Labarin Kuma Gwamnatin jihar Kano ta bayar da umarnin rushe wani haramtaccen gini a gaban gidan Sheikh Nasiru Kabara cikin gaggawa.
Gwamnan jihar, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bayar da umarnin hakan bayan bincike ya nuna cewa ba a taba bayar da izini a hukumance ba kan ginin walau daga Gwamnati ko Masarautar Kano.
Hon. Baffa Babba Ɗan’agundi, shugaban hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta Kano, KAROTA, wanda ya zama shugaban kwamitin kawar da haramtattun gine-gine shine ta sanar da hakan a wata Sanarwa da aka tanada manema labarai ta hannun mai magana da yawun hukumar Nabilisi Abubakar Kofar Na’isa.
”Yana da kyau jama’a su sani cewa wannan haramtaccen ginin ya janyo cece-kuce tsakanin gwamnatin jihar da Masarautar wanda duk da cewa dayan bangaren na da hannu a ciki amma bayan da aka yi bincike aka gano cewa wasu masu son zuciya da son rai ne kawai suka shige gaba wajen aiwatar da hakan.
Yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike, Gwamna Ganduje ya bayar da umarnin rushe gaba daya, ginin shagunan da aka fara.
A don haka za a ci gaba da barin wajen ga kungiyar Kadariyya da ke amfani da shi wajen yin zikirin.
Gwamnan ya kuma bayar da umarnin a samar da jami’an tsaro 24/7 a yankin domin kare matasan da kan yi amfani da filin wajen wasanni kala kala.