By Abbas Yakubu Yaura
Wasu bayanai da aka samu daga rajistar cibiyoyin lafiya na ma’aikatar lafiya ta tarayya sun nuna cewa Najeriya na da asibitoci masu aiki 40,017 kacal a fadin jihohi 36 na tarayya da kuma babban birnin tarayya FCT.
Cibiyoyin kiwon lafiya mallakar gwamnati ne sai kuma asibitoci masu zaman kansu na hadin gwiwa.
An lura cewa jihohin Bayelsa, Borno da Ekiti ne ke da mafi karancin asibitoci da wuraren shan magani a kasar nan.
Bisa ga bayanan, 10,655 na kayan aikin ana gudanar da su a asirce kuma sun kasance a kan matakan kulawa daban-daban; wato matakin farko, da mataki na biyu zuwa babban mataki na uku.
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa a jihohi kamar Bayelsa, Borno, Ekiti, FCT, Gombe, Ribas, Yobe da Zamfara, adadin asibitoci da dakunan shan magani bai kai 800 ba.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa jihar Legas ce ta zo ta daya wajen yawan asibitocin da suke aiki, an lura cewa 1,875 daga cikin 2,333 masu aiki na asibitoci da dakunan shan magani masu zaman kansu ne, wanda ya bar cibiyoyi 458 a karkashin gwamnatin tarayya, jihohi da kananan hukumomi.
Jihohin da ke da kayan aikinsu daban-daban sun hada da, Abia tana da 1,196, Adamawa guda 906, Akwa Ibom 818; Anambra 1,166, Bauchi 1,225, sai Bayelsa 311, jihar Benue 1,837, Borno 539, Cross River 1,280, Delta 821, Ebonyi 830, Edo 1,042, Ekiti 570; Enugu1,037, tare da birnin tarayya FCT mai guda 767, da kuma Gombe mai guda 671.
Sauran su ne Imo 1,197, Jigawa 769, Kaduna 1,419, Kano 1,476, Katsina 1,942, Kebbi 956; Kogi 1,235; Kwara 995; Legas 2,333; Nasarawa 1,357; Neja 1,565; Ogun 1,197; Ondo 823; Osun 1,067; kazalika jihar Oyo tana da 1,490; Filato 1,470; Rivers 586; Sokoto 841; Taraba 944; Yobe 585; da kuma jihar Zamfara mai guda 777.