Tsohon shugaban kasa Olusegun Aremu Obasanjo ya yi gargadin cewa Najeriya za ta ci gaba da zama cikin halin rashin tsaro rashin ci gaba da tabarbarewar al’amura muddin aka ki sauya fasalin yadda ake tafiyar da kasar yanzu haka.
Obasanjo ya ce duba da yadda nauyi ya yi wa Gwamnatin tarayya yawa musamman ta bangaren tsaro, sauya tsarin shugabancin kasar ya zama wajibi.
Ya fadi hakan ne yayin wata lacca da aka saba gudanarwa duk shekara ta Sobo Sowemimo da ta gudana ta fasahar bidiyo a birnin Abeokuta na jihar Ogun.
Taken laccar ta bana dai da wata kungiya mai suna Abeokuta Club ta shirya shi ne, “COVID-19: Ina mafita ga kalubalen tsaron Najeriya?”.
Obasanjo wanda ya zargi gwamnatoci a dukkanin matakan Najeriya da gazawa ya ce yanzu ba lokacin da za a zauna a ci gaba da kallon abubuwa na kara tabarbarewa ba ne.
Obasanjo ya yi kira ga faɗin shugabannin kasar nan da su maida hankali wajen kawo karshen matsalar tsaro da ayyukan ta’addanci, sannan kuma da maida hankali wajen samar da abinci da ayyukan yi ga matasa domin gujewa shiga matsalar yunwa bayan fita daga annobar Korona.