Gwamnan jahar Lagos Babajide Sanwa-Olu yace Jahar dama Najeriya nada dukkanin abinda ake buƙata domin haɓɓaka Tattalin Arzikin da ake samu a Jahar ta hanyar yawon buɗe ido, Al’adu da kaɗe-kaɗe.
Ya bayyana haka a lokacin da ya jaddada ƙudirin sa na inganta Al’adu a yanzu da kuma shekaru masu zuwa nan gaba.
Ya bayyana baza’a taɓa cimma wani cigaba a kowace al’umma, ba tare da sanin minene al’adar ta ba, yana mai ƙara dacewa ƙasar Najeriya Allah ya Albarkace ta da yawan mutane da arziƙin ƙasa, idan har akayi kyakkyawan amfani dashi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Borno Tace Ta Bada Fifiko Kan Ilimin ‘Ya’ya Mata – Kwamishiniya
Sanwa-Olu ya bayyana haka a lokacin bikin murnar ranar Asa Day ta shekarar 2021 da kuma ƙaddamar da cibiyoyin tallafawa matasa, wanda ya gudana a ɗakin taron na De Blue Roof na gidan talabijin ta Lagos, dake kan hanyar Lateef Jakande, a Agidingbi Ikeja, Lagos.
Taron wanda aka laƙabawa take da “muyi amfani da al’adar da muka gada domin inganta tattalin arzikin mu, wanda ASA day ta Shirya haɗin gwuiwa da Ma’aikatar Yawon buɗe ido, Al’adu ta Jahar Lagos.
Gwamnan ya samu wakilcin Kwamishinar yawon buɗe ido Al’adu Mrs Uzamat Akinbile-Yussuf.
A jawabinshi Oyatoye yayi kiran haɗin kai tsakanin Gwamnati da ƙungiyoyin da bana Gwamnati ba, wajen gano dukkanin abubuwan da ma’aikatu zasu iya samar wa, yana mai jaddada cewa arzikin ƙasa dana mutane zai haɓɓaka idan aka yi amfani da wuraren yawon buɗe ido.