By Abbas Yakubu Yaura
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana cewa za a fara aiwatar da sabon tsarin haraji kan taba sigari daga ranar 1 ga watan Yunin 2022.
Darakta a ma’aikatar kudi ta tarayya Fatima Hayatu ce ta bayyana hakan a wani taro da cibiyar kare hakkin jama’a ta Civil Society Legislative Advocacy Center (CISLAC) ta gudanar.
Manajan Shirye-Shirye kan Mulkin Dimokuradiyya, Okeke Anya ya jagoranci kungiyar Ayyukan Harajin kan Taba Sigari.
Hayatu ta kira sana’ar tabar sigari a matsayin mai karfin gaske, inda ta bada tabbacin ma’aikatar ta himmatu wajen ganin an tabbatar da cewa hajar ta shigo kasuwa.
Ta yi nuni da cewa, ana shirin shiga tsakanin masu ruwa da tsaki domin aiwatar da ingantaccen tsarin bin diddigi.
Gwamnati za ta kafa wata kungiya mai aiki da harajin taba don yin nazari kan abubuwan da sauran kasashen ECOWAS ke yi.
Daraktan ya ce harajin kan sandar sigari daya ya kai Naira 2 da kobo 90 amma yanzu ya karu zuwa Naira 4 da kobo 20.
Hakan ya biyo bayan shawarar da ECOWAS ta bayar na kashi 0.02 akan kowacce sandar sigari wanda a halin yanzu farashin zai ba da Naira 8 da kobo 40.
“Duk da haka, an amince da biyan shawarar rabin hanya wanda zai ba da Naira 4 da kobo 20 daga cikin wannan shekarar 2022.
“Sai kuma a shekarar 2023, za a kara 50kobo da za a samu Naira 4 da kobo 70 sannan a shekarar 2024, za a kara kobo 50 ya zama Naira 5 da kobo 20.
“Waɗannan duka za su nuna haɓakar Ad Valorem na yanzu daga kashi 20% zuwa 30%. Wannan karuwa ne a hankali a cikin haraji, kuma duk a halin yanzu ana nazari.
“Ƙara harajin ba kawai na kayan sigari ba ne, amma ga wasu kamar shisha, nau’in na’urorin da ake amfani da su don kai da cinye su.
“Za kuma a rika biyawa Shisha harajin Naira 3,000 a kowace lita, naira 1,000 kan kowace Kg kuma za a rika kara masa harajin naira 500 duk shekara,” Hayatu ta bayyana.
A nasa jawabin, Anya ya bukaci Gwamnatin Tarayya da ta sanya tukwanen Shisha da sauran na’urorin shan taba na lantarki a cikin sabon tsarin harajin taba.
Jami’in na CISLAC ya ce hakan zai kawo cikas ga bukatarsu da kuma kara samun kudaden shiga ga al’ummar kasar.
“Taba yana da mummunar tasiri ga lafiyar ‘yan Najeriya”, ya jaddada cewa ya kamata a biya shi da kyau a matsayin kayan alatu.
“Ƙarin harajin zai zama wata hanya ta samar da kudaden shiga. Wannan shi ne yadda kasashe da yawa ke aiki saboda shan taba abin jin dadi ne ba larura ba,” inji shi.
Anya ya dage cewa ‘yan kasar za su so sanin kayayyakin taba da suka biya harajin da ya dace da kuma inda suka zo.
Comments 1