Wata Babbar Kwamishinar Kasar Landan Catriona Laing a ranar Litinin a Benin ta bayyana fatan cewa Najeriya zata magance matsalolin tattalin arziki da tsaro data ke fama a Kasar.
Laing ta bada tabbacin haka a lokacin da take jawabi a taron liyafar cin abinci da aka shirya domin karrama ta.
KARANTA WANNAN LABARIN: Tsohon Gwamnan Edo Igbinedion ya rasa Mahaifiyarshi mai shekaru 85
Acewar ta, “ina da tabbacin cewa Najeriya zata samu mafita a wannan lokaci na matsatsi, da ake fama da matsalar tsaro
” ni mai fata ce ga Najeriya, kuma ina tunanin Edo zata jagoranci Najeriya zuwa inda ya kamata taje, kuna da Gwamna dayake damuwa akan abubuwan da suke faruwa, kuma ina jindadin haka.
A jawabin shi, Gwamna Godwin Obaseki ya godema Babbar Kwamishinar Kasar Landan a Najeriya da irin goyon baya ga Jahar wanda ta dade tana samu.