Nan ba da jimawa ba za mu fallasa sunayen Manyan Mutane masu Satar Mai – Garba Shehu
Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, Malam Garba Shehu, ya ce nan ba da dadewa ba Gwamnatin Tarayya za ta bayyana sunayen wasu muhimman mutane da ke haddasa satar man fetur a ƙasar nan.
Shehu ya ce, a wani bangare na kokarin tabbatar da tattalin arzikin kasar nan daga zagon kasa, jami’an tsaro sun kai samame a wuraren da ake samun fashe bututun mai.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yadda wata mata ta hallaka Shugaban Ofishin ta kan yunƙurin cin zarafin ta
Da yake magana a gidan talabijin na Trust TV’s a Shirin Siyasar mu a yau, Shehu ya yi ishara da cewa za a iya samun wasu jami’an tsaro da suka aikata wannan haramtacciyar hanya, sai dai ya ce ana daukar sabbin matakan dakile lamarin.
“Ana magance matsalar satar mai. Babbar matsalar da muke da ita a kasar nan ita ce, ya kamata mu kara ganin jajircewa daga al’umma wajen taimaka wa jami’an tsaro. A wasu lokuta, inda wasu a cikin jami’an tsaro suka haɗa baki, da wasu manyan ƙasa” inji shi.
Ya kara da cewa abin kunya ne ga Najeriya rashin cika kason da kungiyar kasashe masu arzikin man fetur ta OPEC ta ba ta.
“Mun kasance muna yaki da OPEC don samun karin kaso; yanzu, sun ba mu kuma ba za mu iya haɗawa ba. Wannan abin kunya ne. Hukumomin tsaro sun ba da gudummawa sosai wajen dakatar da wannan aiki. Ina fata nan da ’yan kwanaki masu zuwa ofishin mai ba da shawara kan harkokin tsaro zai gabatar wa kasar nan, manyan mutane masu tallata irin wannan sana’a yayin da ake kama su da kuma tayar da bama-bamai.
“Kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC) Limited kuma yana sanya ido don gano ko lokacin da ake lalata bututun Mai,” in ji shi.
Dangane da rashin tsaro kuwa, Shehu ya ce kawo karshen tada kayar baya a yankin Arewa maso Gabas shi ne abin da shugaban kasa ya sa a gaba a lokacin da ya hau mulki kuma an yi kokari sosai wajen dakile wannan matsala. Ya kara da cewa ‘yan ta’adda ba su sake yin ikirarin amshi wani yanki ba saboda karfin sojojin Najeriya.