Nan bada jimawa ba zaku ji daga gare mu kan ƙara wa’adin rajistar Katin Zaɓe — INEC
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta INEC ta baiwa ƴan Najeriya tabbacin cewa, zasu ji daga gare ta kan kiraye-kirayen da ake yi na ƙara wa’adin rajistar Katin Zaɓe.
Shugaban Hukumar Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi a wani taron siyasa a Lagos.
KARANTA WANNAN LABARIN: Tsaro: Yan Garkuwa Da mutane Sun Sace Matasa 15 a Jihar Imo
Da ake yaɗa hoton Yakubu a taron, a wani saƙo da aka wallafa daga shafin INEC a ranar Asabar yace “munji kiraye-kirayen ku da Babbar Murya. Nan bada jimawa ba zaku ji daga gare Ni akan ƙara wa’adin rajistar Katin Zaɓe.
“Ku bani tabbacin cewa zaku ji rajista, zaku karɓi katin ku, ni kuma ina baku tabbacin cewa za’a ƙidanya ƙuri’un ku”.
Yin Rajistar Katin Zaɓe za’a daina shi a ranar 30 ga watan yunin Shekarar 2022, amma ana cigaba da yin kira kan ƙara wa’adin kwanakin.
Comments 1