Gwamnan Jihar Wike Ribas, Nyesom Wike, ya bayyana shirin sa na yin magana kan rikicin fidda Gwanin da ya barke a jam’iyyar PDP bayan zaɓen Shugaban Ƙasa.
Ya ce nan ba da jimawa ba zai yi magana kan Ɗan Takarar Jam’iyyar, Atiku Abubakar, domin tabbatar da ƴan Nijeriya sun san gaskiyar abubuwan da ke faruwa a cikin jam’iyyar PDP.
A ranar 28 ga watan Mayu, Atiku ya doke Wike da sauran masu neman tsayawa takarar Shugaban Ƙasa a jam’iyyar PDP da aka gudanar a Abuja.
Wike wanda aka so ya kasance abokin takarar Atiku shima ya sha kaye a hannun Gwamnan Jihar Delta, Ifeanyi Okowa.
Tuni dai Gwamnan Ribas ya rufe bakinsa kan rikicin da ya biyo bayan zaben fidda gwani.
Hakabzalika ya gudanar da tarurruka da dama da shugabannin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da sauran jam’iyyu, inda ya nuna damuwarsa kan makomarsa da babbar jam’iyyar adawa ta Najeriya.
A wata hira da yayi da ARISE TV, Atiku ya ce bai zabi Wike a matsayin abokin takararsa ba saboda yana son wanda zai yi aiki da shi cikin aminci.
“Ba a ki amincewa da Gwamna Wike ba. Babu wanda aka ki amincewa a jam’iyyar. Amma dole ne ku fahimci cewa haƙƙin Ɗan Takara ne ya zaɓi abokin takararsa – wanda ya yi imanin zai iya yin aiki tare cikin lumana, sannan kuma ya fitar da manufofin jam’iyyar, da kuma kokarin hada kan kasar.
“Gwamna Wike hazikin ɗan siyasa ne. Yana da ƙarfin hali, mai jajircewa. Na yi imani yana da makoma a juyin siyasar kasar nan. Ba batun kin amincewa ba ne. Tabbas, a’a. Ina ganin abu ne mai tsauri da za a ce mun ki amincewa da gwamna Wike,” in ji Atiku.
A wata dabara da ya mayar da martani ga hirar Atiku, Wike a wata sanarwa da mai taimaka wa kan harkokin yada labarai, Kelvin Ebiri ya fitar, ya ce ‘yan Najeriya za su san gaskiyar abubuwan da suka faru a jam’iyyar a baya-bayan nan idan ya yi magana.
“Akan Atiku, zan yi magana nan ba da jimawa ba kuma ‘yan Najeriya za su san gaskiyar duk abin da ya faru a PDP a ‘yan kwanakin nan,” Wike