Jiya Talata, Shugaban karamar hukumar Giwa Alhaji Abubakar Lawal Shehu Giwa, da tawagar sa suka ci gaba da kewayen ayyukan raya kasa dana inganta rayuwar Al’umma wadanda ya samar a shekarar farko da yayi a kan kujerar jagoranci.
Da yake tattaunawa da manema labaru shugaban ya ce, tuntuni ya saka a ran shi cewar koda kudaden Local Government, zasu kare kwatakwata sai ya tabbatar ya kammala ayyukan daya yayi kudirin samarwa Al’ummar da yake jagoranta.
Babban dalilin zagayen shine, ya kewaya da kan shi ya tabbatar da ingancin ayyukan tare da jin korafe korafen mutanen sa game da ayyukan, a lokaci guda kuma ya kuma tambayar su wadan su abubuwan da suke bukatar ganin yayi musu.
A nashi bangaren shugaban shashen kula da kudade DPM Idiris Bawa, ya ce shi tunda yake bai taba ganin jajirtaccen mutun kamar Abubakar Lawal Shehu Giwa ba, shi fa daka taba kudaden karamar hukuma gwara ka yanki naman jikin sa.
Ya kara da cewa yana da yakinin nan da Shekaru 100 sai Saar gaske karamar hukumar Giwa ta sami Shugaba kamar Abubakar Lawal.
Jaridar Dimokuradiyya.