Shahararriyar yar wasan Tennis din nan lamba biyu a duniya Naomi Osaka ta fice daga gasar French Open dake gudana a halin yanzu sakamakon ruɗani da aka samu na ƙin tattaunawa da manema labarai.
A jiya Lahadi ne mashirya gasar suka fitar da wata sanarwar haɗin gwiwa kan cewa za a hukunta Matashiyar yar wasan muddin ta ci gaba buna dabi’ar ƙin tattaunawa da yan jarida.
A makon da ya gabata ne matashiyar yar shekara 23 ta kauracewa manema labarai a wani mataki na kare Lafiyar Ƙwaƙwalwar ta, lamarin da ya kai ga a yau ta ce za ta jefar da kwallon mangwaro don hutawa da ƙuda.
Wani sako da ta wallafa a shafin ta na tuwita, Osaka ta ce ta gamu da matsalar damuwa tun bayan da ta lashe gasar Grand Slam a shekarar 2018.