By Abbas Yakubu Yaura
Likitocin dake aiki tare da Gwamnatin Jihar Nasarawa sun roki Gwamna Abdullahi Sule daya duba yiwuwar kara musu alawus alawus daga naira 5,000 zuwa naira 100,000 duk wata.
Likitocin sun bayyana damuwar tasu ne biyo bayan rasuwar wasu kwararrun likitocin mata, Nwaru Victor da Esa Oga, wadanda suka rasu kwanan nan sakamakon cutar zazzabin Lassa, bayan sun kamu da cutar daga wata mace mai ciki data kamu da cutar, wadda aka garzaya da ita Asibitin kwararru na Dalhatu Araf dake Lafiya domin neman haihuwa, amma daga baya ta rasa ranta tare da jaririn data haifa.
Da yake jawabi a ranar Talata, Shugaban kungiyar likitocin Najeriya a jihar, Dakta Emmanuel Sabo, ya bayyana cewa kudaden alawus din hatsari na naira 5,000 duk wata bai wadatar ba sakamakon kasadar dake tattare da sana’ar.
Sannan ya ce, “Likitocin kiwon lafiya na fuskantar babban hatsari a kullum yayin gudanar da ayyukansu. Muna yin aikin ne saboda muna son shi, musamman saboda ya shafi ɗan adam. Mun san cewa gwamna yana yin iya kokarinsa a gare mu da sauran jama’a a fannin lafiya, amma muna rokon a kara mana.
“Naira 5,000 na alawus alawus na hatsari duk wata bai ishe mu ba. Za mu yi farin ciki idan Gwamna Abdullahi Sule ya yi amfani da kyawawan ofisoshi ya kara mana shi ya koma zuwa Naira 100,000 domin likitocin jihar su samu biyan bukatunsu na yau da kullum na kudi.”
Ya kuma yi kira ga gwamnan daya bayar da tallafin karatu ga yaran mamatan da suka bari, domin matansu ba za su iya sauke nauyin tarbiyyar yaran ba.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa A nasa bangaren, babban daraktan kula da lafiya na DASH, Dakta Hassan Ikrama, yace rashin likitocin biyu babban bala’i ne ga asibitin.
Kazalika Ya bayyana cewa wadanda suka mutun sun sadaukar da kansu sosai wajen gudanar da ayyukansu da kyautatawa ga wadanda suka yi aiki tare dasu.