Sanata uba sani Mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya a majalisar dattijan Nageriya ya gabatar kudurori kamar haka, domin cigaban ƙasar nan.Kudurorin sun hada da:
KUDURI NA FARKO
1. Kwalejin Ilimi ta Tarayya a karamar hukumar Giwa dake Jihar Kaduna, Wanda Sanata Uba Sani ya gabatar a shekarar 2019:
An gabatar da Kudirin ne, duba da ganin babu yadda za a iya farfado da ingancin Ilimi, matukar ba a ba bangaren samar da kwararrun malamai mahimmanci ba, kuma tuni Kudirin ya tsallake karatu na 1 da na 2 a zauren majalisar dattawa.
A ranar 9 ga watan Maris na shekarar 2019 ne, masu ruwa da tsaki a yankin karamar hukumar Giwa, tare da Sanata Uba Sani, su ka kaddamar da taron jin ra’ayoyin jama’a, wanda kwamitin kula da karatun gaba da sakandare, da asusun tallafa wa manyan makarantu TETFund su ka shirya.
Kudirin, ya tsallake karatu na uku a zauren majalisar dattawa a ranar 15 ga watan Yuli na shekara ta 2020, an kuma karanta shi karo na farko a zauren majalisar wakilai a ranar 3 ga watan Disambar shekarar 2020, don haka yanzu majalisar wakilai kawai ake jira, ta kammala nazarin ta a kai, kafin a mika shi ga shugaban kasa, ya sanya ma shi hannu.
KUDURIN MALLAM UBA SANI NA BIYU
2. Asibitin Tarayya na garin Rigasa, dake garin Kaduna a shekarar 2019:
An gabatar da wannan kudiri ne, sakamakon korafe-korafen al’ummomin yankin, dangane da yadda ake samun yawaitar mace-macen mata da kananan yara, saboda rashin igantattun kayayyakin duba lafiyar marasa lafiya a cibiyoin kiwon lafiya.
Samar da Cibiyar, zai sa a samu sauki ta fuskar kula da ayyukan tiyata, da masu fama da cututtukan da su ka hada da Ciwon Zuciya, da Cutar Daji, da cututtukan da su ka shafi Kashi, da hanci da Kunne da Makogwaro, da gyambon Ciki, da dai sauran cututtukan da su ka fi damun al’ummomin Nijeriya.
A ranar 18 ga watan Fabrairu na shekara ta 2019, masu ruwa da tsaki na yankin Rigasa, sun ka halarci taron jin ra’ayoyin jama’a a kan kudirin, wanda kwamitin Lafiya na majalisar dattawa ya shirya.
Tuni dai kudirin ya tsallake karatu na uku a zauren majalisar Dattawa a ranar 3 ga watan Disamba na shekara ta 2020, wanda majalisar Wakilai kawai ake jira, kafin a mika shi ga shugaban kasa ya sanya ma shi hannu.