By Ishaq Dabai
Sama da magidanta 48,000 ne suka amfana da shirin gwamnatin tarayya na bada kudi a hannu karkashin shirin samar da hannun jari na NSIP.
Babban mai baiwa gwamna shawara na musamman Abdullahi A Sule da jinkan ma’aikata Hon Imran Usman Jibrin ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a yayin gudanar da bikin bude shirin a kananan hukumomin dake fadin jihar ta Nasarawa.
Hon Imran yace shugaban kulada shirin na bayar da hannun jari na jihar yace zasu biya naira 30,000 na tsawon wata shida ga wadanda suka amfana da shirin na bada kudi a hannu a jihar inda suka biya sama da mutane 48,000 a fadin jihar.
Baya da haka ya nuna jin dadinsa ga ministan jinkai da da walwalar jama’a Hajiya Sadiya Umar Faruq bisa kawo shirin cikin jihar.
Acewar Imran jihar Nasarawa tana daya daga cikin jihohi da aka fara gabatar da shirin na gwamnatin tarayya na bada kudi a hannu inda ake biyan naira 5000 duk wata ga wadanda suka amfana da shirin a kananan hukumomin 13 dake fadin jihar, gwamnan yace za’a fadada shirin na NSIP wajen rubanya shi a cikin jihar.
Sannan yace tsarin shirin shine a kawar da talaucin da magidanta suke fama dashi inda a ke biyansu naira 5000 duk wata kimanin dala 12.6 kenan, ya kuma bukaci wadanda suka amfana da shirin da suyi amfani dashi wajen ciyar da jihar gaba.