NASU, SSANU sun ƙara wa’adin Yajin Aiki da watanni biyu
Gamayyar Kwamitin Ƙungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’o’i, da Ƙungiyar Ma’aikatan Jami’o’i, da ire-iren su, sun tsawaita yajin Aiki da watanni biyu masu zuwa.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Shugaban Ƙungiyar SSANU Mr. Mohammed Ibrahim Sakatare-Janar Mr. Peter Adeyemi suka sanyawa hannu.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu-Yanzu: Bayan Tururuwar Ficewa Daga APC, Shugaban Jam’iyar Na Ganawa Da Sanatocinta
Sanarwar tace “duba da yadda Gwamnati ke jan ƙafa wajen shawo kan Matsalolin su dake a ƙasa, zata bada dama a kammala biyan buƙatun su kafin janye yajin aiki ba. A saboda haka, muke sanar da kara wa’adin Yajin aikin mu da watanni biyu, inda muke fatan cewa za’a shawo kan Matsalolin mu. Kuma wannan ƙara wa’adin Yajin aiki zai fara ne daga ranar Juma’a 24 ga watan yunin Shekarar 2022.”
Majiyar mu ta bayyana cewa, SSANU, da NASU sun fara yajin aiki ne da yajin aikin gargaɗi wanda ta fara a daren ranar Lahadi 27 ga watan maris na Shekarar 2022, daganan ta ƙara wa’adin da makonni biyu, shima ya fara daga ranar 10 ga watan Afrilu na shekarar 2022, kuma har yanzu ake cigaba da yi.
Wasu daga cikin buƙatun su, sun ƙunshi maganar manhajar biyan Albashi ta IPPIS, kuɗin Alawus-Alawus, da yarjejeniyar Gwamnatin Tarayya da NASU, SSANU, da sauran wasu buƙatu
Comments 1