Kwamitin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar APC, PCC, ya bayyana kwarin gwiwar cewa amfani da tsarin tantance masu kada kuri’a na BVAS, zai taimaka wajen kawar da siyasar kudi a zaben Najeriya.
Festus Keyamo, mai magana da yawun kwamitin PCC ne ya bayyana hakan a lokacin ganawarsa da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN a Abuja ranar Lahadi. Daily Post ta ruwaito.
KU KARANTA: EFCC Ta Kwato Naira Miliyan 900 Na Shirin NHIS
Karamin Ministan Kwadago da Ayyuka ya kuma yabawa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) bisa bullo da tsarin watsa sakamakon zabe ta hanyar intanet, kai tsaye daga rumfunan zabe.
Ya ce da bullo da fasahohin biyu a cikin zabukan Najeriya, a lokacin da ake biyan jami’an zabe da jami’an tsaro kudaden da za su canza sakamakon zabe a wuraren tattara sakamakon zabe.
Ya ce kafin yanzu, ana amfani da kudi wajen baiwa jami’an tsaro da jami’an zabe cin hanci don sauya sakamakon zabe, amma BVAS za ta kawar da hakan.
Keyamo ya bayyana BVAS a matsayin alheri ga tsarin zaben Najeriya.
A wani labarin kuma: Zaben 2023: Hukumar INEC Ta Bayyana Wadanda Zasu Yi Aiki Da Na’urar BVAS
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana shirinta na gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da za a yi ranar Asabar.
Hukumar ta kuma dage kan cewa mambobin dake hidimar kasa ne, kawai za su gudanar da tsarin tantance masu kada kuri’a ta hanyar amfani da na’urar BVAS a lokacin zaben.