Rahotannin sun tabbatar da cewar jami’an tsaro sun garkame Kansilar gundumar Afaka da mukarrabansa bayan da ake zarginsu da yin awon-gaba da na’urar taransafomar (transformer) wutar lantarki har guda shida mallakin gundumar Afaka.
Kafin yanzu tsohon dan majalisar wakilan tarayya Honorabul Abubakar Mamadi, ne ya samar da taransafomar guda shida domin cima alkawuran da ya dauka lokacin yakin neman zabe. Ya kuma danka amanar su ga Kansilar gudumar Afaka Auwalu Muhammad wanda aka fi sani da (Koraye), kuma aka ajiye su a harabar tsangayar koyar da Sanao’i dake jikin ofishin ‘yan sanda dake kusa kasuwar Mando a Kaduna.
Akwai tabbacin cewar tun daga hanya taransafomar guda 2 daga cikin 6 suka yi batan-dabo, sama ko kasa, yayin da aka kai guda 4 aka ajiye, tsawon lokaci suna ajiye. Auwalu Koraye yaki yarda a sanyawa al’umma taransafomar duk lokacin da aka bukata sai ya kawo wani uzuri har ta kai ta kawo al’umma suka fara cewa a ba su za su dauki nauyin sakawa da kansu.
Bayan tsawon lokaci, Koraye da ‘yan fadarsa da suka hadar da Jume da Bomboi da Sulaiman da Na’u, sun yi tunanin cewar an manta kowa ya hakura gashi kuma Mamadi, daya bayar da tiransfomar ya sauka bashi data cewa, kawai sai suka cefanar da su duk kuwa da irin kalubalen rashin wuta da kuma rashin isassun tiransifomomin da yankin ke fuskanta.
Matsalolin rashin Wuta da kalubalen taransafomar ya kara tsamari a gundumar Afaka wanda hakan yasa aka matsa kan maganar taransafomomin, hakan ya saka aka waiwayi inda aka ajiye su kuma aka neme su aka rasa. Wakilan yankin tuntubi sun Auwalu Koraye, domin jin ba’asin inda suka shiga, bayan da ya rasa ta cewa sai ya shiga neman tashin hankali daga nan ne aka tura maganar gaban hukuma domin gabatar da bincike.
Ko da hukumar ‘yan sanda ya shiga bincike sai ta gana babu taransafoma ko daya a ajiye hakan ne ya tilasta hukumar kama Auwalu Koraye gami da yaransa kuma shugaban hukumar ‘yan sanda na yankin ya hana bada belinsu. Wannan ne ya tilastawa Koraye neman taimako daga wajen shugaban karamar hukumar Ighabi Jabiru Khamis wanda shi ne yayi ruwa yayi tsaki har aka samu bada belinsu bisa sharadin dawo da na’urar taransafomar.
Jama’ar yankin sun kafa kwamitin mutane bakwai daga kowane yankin wakila domin ganin an dawo da na’urar.
Sai dai Koraye na gudun kar maganar taje kunnen iyayen gidansa a siyasa don kar sunansa dana yaransa ya baci.
Wani mazaunin yankin mai suna Shuaibu Abudllahi yace ba zai bayyana sunayen wanda suka sayi na’urar ba har sai kwamitin sun kammala bincikensu.