Na’urorin mu ba na sayarwa bane, KEDCO
Hukumar dake da alhakin rarraba wutar lantarki a Jahar Kano, ta sanar da mutane cewar na’urorin da ma’aikatan ta ke sanyawa kyauta ne ba na sayarwa ba ne.
Mista Ibrahim Shawai ya sanar da hakan a wani bayaninsa a rana Litini a Kano, yace ya zama dole a yima mutane bayani domin ikirarin da wasu keyi a kafar sada zumunta suna cewa masu amfani da na’ura zasu biya.
KARANTA:- Jami’an NCDSC na bukatar hadin kan Yan Najeriya domin inganta tsaro
Yace wannan ba haka bane, bamu taba karbar kudi kan na’urar ba, ko wajan sanya ta.”
Shawai yace “duk wanda aka kama ko da daya daga cikin ma’aikatan mune hukunci zai tabbata kansa kamar yadda aka tanadar.”
Ya cigaba da bayani in da yace masu amfani da wutar dai sun kawo mana bayani babu daya daga cikin ma’aikatan mu dake karbar kudi wajan sanya na’urar kawo yanzu.
Malam Nasiru Danmaraya, mazaunin Sheka a Jahar Kano ya tabbatar da an sanya masa batare da karbar kudinsa ba.
Haka shima Mista Bello Yusuf mazaunin Salanta shima dan garin Kano, shima yace “bai bada ko sisi ba domin ba wanda ya bukaceshi dayin haka.”
Ya Kuma ce “wannan abune mai kyau, na yabawa gwamnatin tarayya da kuma hukumar KEDCO, idan hakan ya tabbata zai rake korafe-korafe akan takardar wuta.”
Comments 1