Wani dan Najeriya ya kwana a gaban ATM kasancewar yana son zama mutum na farko da zai ciri kudi da safe, Intelregion.com ta ruwaito.
Tun bayan sakin sabbin kudade, ‘yan Najeriya suna ta fama kan yadda za su samu damar cire kudi don amfanin rayuwa.
KU KARANTA: Saka rigar bacci asarar lokaci ne saboda da safe za kin tsiceta a ƙasa, Fasto ga matarsa
Nan da nan wasu bidiyo suka hau yawo a kafafen sada zumuntar zamani inda aka ga ‘yan Najeriya suna ta dambe da iyayyaku kala-kala.
Yayin kokarin kasancewa na farko wurin cirar kudi da zarar safiya ta yi, wani dan Najeriya ya kwana gaban ATM.
A bidiyon wanda aka gani yana yawo a kafafen sada zumunta an ga yadda ya kwanta ya baje gaban ATM din inda ya daga kafarshi daya a jingina jikin bango.
Nan da nan mutane suka hau sharhi karkashin bidiyon ko wanne yana korafi kan yadda rayuwa ta zama cikin kunci tun bayan sauya kudaden.
Yadda Jariri Ya Sheki Bacci, Bayan Mamansa Ta Saka Shi Cikin Abin Wasa, Bidiyon Ya Dau Hankali
Masu amfani da kafar sada zumunta ta TikTok guda dubu 59k sun ji daɗin bidiyon jaririn da ya yi barci a cikin wani abun wasan yara lokacin da mahaifiyarsa ta saka shi a cikin don yin tsalle, Legit.ng.
Bidiyon ya nuna yaron yana sharar bacci sosai inda mahaifiyarsa ta sanya shi a cikin abin wasa lokacin da ba ta daki dan debe masa kewa.
Masu amfani da TikTok suna magana game da jaririn a cikin sashin sharhi tare da wasu da ke bayyana abubuwan da suka faru da yaron.
Masu amfani da TikTok suna mayar da martani ga bidiyon jaririn da ya yi barci a wani wurin wasan yara.