Shugaban kwamitin yaki da cin hanci na fadar shugaban kasa Farfase Itse Sagay (SAN) ya bayyana mamakin game da ikirarin da ake cewa wai Shugaban ƙasar Najeriya ƙarƙashin mulkin soja Janar Sani Abacha bai saci kudi daga asusun gwamnati ba.
Dukkanin kuɗaɗen da aka dawowa da Najeriya daga ƙasashen ketare, amma mai dakin marigayi Abacha, Maryam Abacha ta bada tabbacin cewa mijinta bai saci dukiyar Najeriya ba.
Maryam ta bayyana cewa abun kunya ne ga shugabannin Najeriya, suke yiwa matacce kazafi bayan ya share shekaru 22 da rasuwa.
https://dimokuradiyya.com.ng/amurka-ta-maido-wa-najeriya-dala-miliyan-311-na-abacha/
Sai dai a yayin tattaunawarsa da jaridar Punch, Sagay ya bayyana cewa yayi mamaki da har yaji akwai wanda zai iya fitowa ya karyata gaskiyar satar kudaden da Abacha ya yi.
“Abun mamaki a nan shi ne duk kuɗaɗen da aka dawo da su, suna so suce kuɗaɗen albashi ne ko kuma na kadarorinsa ne dake kasashen waje, wannan abun kunya ne ace akwai wanda zai fito ya daki kirji cewar Abacha bai yi sata ba”. Cewar Farfesa Sagay.