Alh. Sani Zangina Daura
A yau dai ba mu san gobe ba, Muhammadu Buhari shi ne mutum ɗaya tilo da yake da muradin ganin ƙasar nan ta ci gaba ta ko wane fanni.
Nayi duba da nazari kan muƙarraban Baba Buhari, sai na hango cewa mafi akasarinsu sun maida hankalinsu ne akan abinda zasu samu da iyalansu maimakon Cika Muradun Jama’a.
Yau muƙarraban shugaba Muhammadu Buhari sun mallaki kadarorin da wanda ya naɗasu mukamin bai mallaka ba, to amma abin tambaya a nan shi ne, shin in aka saukesu aka ɗaukoka kai ko ke mai karatu, shin zaka iya cewa halinka ko naki zai bam-banta da wanda aka sauke ko za a sauke?
Na tattauna da wasu ƴan ƙasa ta Najeriya kan cewa idan Baba Buhari ya kiraka ya baka Amanar Naira Miliyan dari (100,000,000 = 00) cewa ka rabawa ƴan unguwarku, nawa zaka rabawa jama’a?
Mutum na farko yace shi gaskiya ba zai faɗa ba saboda shi yasan tabbas ba zai yi adalci ba.
Na biyu yace in aka bashi abinda zai iya rabawa kowa da kowa shi ne Miliyan biyar (5,000,000 = 00) ya riƙe Milyan 95.
Na uku yace in aka bashi amanar raba Miliyan ɗari kuma ya tabbatar ba za abi bahasi ba to fa lallai ba zai baiwa kowa komi ba kawai dai zai tara ƴan uwansa ne ya masu alheri.
A kaf tattaunawata da waɗanda na tattauna da su, banga wanda zai kamanta adalci ba, kuma fa a hakan waɗannan jama’ar sune dai ke kewaye da Baba Buhari mai gaskiya.
Fatana shine Allah Ta’ala ya ƙarawa Baba Buhari lafiya da nisan kwana yasa ya gama mulkinsa lafiya.
Sai kun ji Ni, A Karo Na Biyu, Alh. Sani Zangina Daura, Ɗan Kishin ƙasa Nagari.