Hukumar da ke lura da gidajen rediyo da Talabijin na Nijeriya, NBC ta bai wa Makarantar kimiyya ta gwamnatin jihar Legas, LASPOTECH lasisin bude gidan rediyo da zai gudanar da aikinsa a mita 101.9FM.
Daraktan yada labarai na LASPOTECH, Olanrewaju Kuye shi ne ya tabbatar da hakan ma ‘yan jarida a garin Legas a yau Litinin.
Kuye ya ce Dr Vincent Chibuike Ogwumike, Daraktan hukumar na Legas shi ne ya mika shaidar lasisin gudanar da ayyukansu ga Shugaban riko na makarantar, Olumide Metilelu.
Sannan har wala yau NBC sun mika musu takardar dokokin hukumar domin ganin sun bi wajen gudanar da ayyukan gidan rediyon.
Kuye ya ce za su horas da ma’aikatan gidan rediyon, inda kuma Metilelu ya tabbatar da NBC din cewa gidan rediyon zai bi dokokin NBC din.