Hukumar da ke Kula da Kafafen Yada Labarai ta Kasa (NBC) ta sanya wa gidan talabijin na Trust TV tarar Naira miliyan biyar saboda yin rahoton binciken kwakwaf kan ayyukan ’yan bindiga.
Gidan talabijin din dai daya ne daga cikin kafafen yada labarai mallakin kamfanin Media Trust, kuma mamallaka jaridun Daily Trust.
Matakin na zuwa ne kasa da mako daya bayan Ministan Yada Labarai da Al’adu, Lai Mohammed, ya yi barazanar cewa Gwamnatin Tarayya za ta hukunta su tare da kafar yada labaran kasar Birtaniya ta BBC, saboda yin rahoton.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa a cikin rahoton kafafen yada labaran sun zanta da yan bindigar, kan halin da suke ciki da kuma dalilan su na kai hare haren kan wadanda basu ji ba, kuma basu gani ba.
DUBA WANNAN LABARIN: Gwamna Buni ya halarci wajen jana’izar kwamishinansa
Sannan kuma sun tattauna da wadanda iftila’in ya faru akan su, tare da irin Neman taimakon mahukuntan da suke.
A rahoton Trust TV, sun zanta da dan ta’addan nan Bello Turji, wanda kuma yake jagorantar ayyukan Ta’addanci, a jihohin Katsina, da Zamfara, da Sokoto.
Yayin da ita kuma BBC ta zanya da rikakken dan ta’adda, Ado Alieru wanda shi kuma yake ayyukan ta’addancinsa ƙauyukan Zamfara.
Hukumar NBC cikin wata Sanarwa da ta aikewa da Kamfanin Media Trust Group, ta bayyana cin gidan talabijin tarar Naira Biliyan 5, sakamakon bayyana ayyukan ta’addancin da yan ta’adda.
Kamfanin dai yace kafin sakin bidiyon, sai da ya tuntubi masana a bangaren, kuma suka basu tabbacin komai yayi daidai babu abinda ya sabawa da ka’ida.