Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC) na gab da fara amfani da Sabuwar fasahar sadarwa ta (5G) a Najeriya.
Tuni dai an ba da lasisin mallakar tururin ga kamfanonin sadarwa, da zasu Yi amfani da shi wajen fara aiwatar da Fasahar wadda Zamani ya zo da ita.
Duk da cewa za a fara aiwatar da Fasahar ne daga manyan biranen jihohi kuma sannu a hankali za a kara zuwa wasu yankuna a fadin jihar, yana da kyau a fahimci cewa, shi wannan sabon Tsarin sun banbanta da hanyar sadarwa ta 1G, 2G, 3G da 4G, Kuma fasahar ta 5G za ta kawo ingantuwar hanyoyin sadarwa da yawa, gami da saurin sadarwa mai girma.
Farfesa Umar Garba Danbatta, mataimakin shugaban hukumar kula da harkokin sadarwa ta Najeriya (NCC), ya bayyana a ranar NCC a yayin bikin baje kolin kasuwanci na Kaduna cewa, “mafi mahimmanci, shi ne kuma alkawarinmu a NCC, mu ci gaba da samar da daidaito a ƙasa don masu aiki don bunƙasawa da haɓaka saka hannun jari da isar da sabbin ayyuka ga masu siye na bai ɗaya, da manyan masu kasuwanci ta hanyar tabbatar da ingantaccen ƙwarewar mabukaci.”
Ya ce a tsawon shekarun da suka gabata, NCC ta ci gaba da zama abokan hulda na KADCCIMA (masu shirya bikin baje kolin kasuwanci na Kaduna) “kamar yadda hukumar ke yin amfani da damar da taron shekara-shekara ke bayarwa don jawo hankalin masu amfani da wayar tarho da masu kasuwanci, wadanda suke a wannan yanki.