Daga Ahmad Umar, Gombe
Hukumar sadarwa ta kasa NCC tace ta kama mutane 200 masu yin rijistar layikan waya ba bisa ka’ida ba a wasu yankunan kasar nan, daga shekara ta 2015 zuwa shekara ta 2019.
Sanarwar hakan ta fito ne ta bakin Mataimakin Daraktan sa’ido da tsawatarwa na hukumar Salisu Abdu, lokacin da yake gabatar da kasida mai taken hadarin dake cikin yin amfani da layikan wayar da akayi rijistar su ba bisa ka’ida ba.
Yayin wani taron wayar dakan al’umma mazauna yankunan Arewa maso gabashin kasar nan akan hadarin dake cikin ayyukan ‘yan Damfara ta hanyar yin rijistar layin waya a garin Gombe.
Salisu ya bayyana cewa hukumar ta NCC zata hukunta duk wani mutum da aka kama da laifin siyar da layin wayar da ba’ayi masa rijista ba.
Kana ya kuma kirayi manyan dilolin saida layikan waya, da kuma cibiyoyin sadarwa da su daina yawan mutanen da suke so su sayar musu da layi a kowace rana, inda yace hakan zai rage yawan samun layikan da ba’ayi musu istaba.
Wasu daga cikin mahalarta taron, Shugaban masu saida wayoyi n arewa maso gabashin kasar nan Isah Babayo, da kuma Sa’adu Umar Yobe, sun yi alkawarin bin dokokin da hukumar ta gindaya musu.