Hukumar dake horas da sana’o’i ta kasa, NDE a ranar Talata ta tallafawa mata 200 a kananan hukumomin Wudil da Garko dake jihar Kano.
Shirin tallafin wanda dan majalisar tarayya mai wakilar Wudil/Garko, Mohammed Ali ya bai wa wadanda suka amfana da shirin da naira dubu goma domin ganin sun bunkasa sana’o’in na su.
Alhaji Iliyasu Ahmed, shugaban NDE din a Kano, ya ce a karkashin shirin an zabo mata 100 ne daga kowanne karamar hukumar guda biyu. A cewarsa, shirin a yankin an shirya shi ne domin tabbatar da cewa sun zama masu dogaro da kansu tare da tallafawa wasun su.
Ahmed ya ce shirin yana karkashin ‘Micro Enterprise Enhancement Scheme’ na gwamnatin tarayya domin rage rashin aikin yi a tsakanin mata da matasa a kasarnan.