Shugaban kungiyar NURTW dake Karamar hukumar Ijaro, Jahar Ekiti, Babatunde Babade, mai kimanin shekaru 45, da lesanmi Shola, mai kimanin shekaru 35, da Babajide Johnson, mai kimanin shekaru 45, sun shiga hannun Jami’an NDLEA kan laifin safarar miyagun kwayoyi. Jaridar Vanguard ta wallafa a shafinta
An cafke shugaban kungiyar ta NURTW ne da kwayar skunk wadda ta kai nauyin kilograms 52.5 a Ekiti babban birnin Ondo, inda ya lodo kwayoyin a matorsa kiran Mazda 1997 koriya, mai lamba Ekiti JER194 AE daga Akure zuwa Ekiti.
Babade, an tafi dashi zuwa magarkama nan take bayan anyi nasarar cafke shi tare da mutanensa su biyu, an tafi dasu a ranar Lahadi da misalin karfe biyu don cigaba da bincike.
KARANTA:- AHMED MUSA zai dauki biliyan daya a duk shekara a kasar Turkiyya
Lokacin da ake tambayarsa cewa yayi motar tasace ta safarar miyagun kwayoyin.
Ya rigada ya bayyana cewa, wasu jami’an tsaro sun cafke motar ne tare da Yan uwansa su biyu, motar na dauke da buhuna takwas na miyagun kwayoyin.
Haka kuma jami’an tsaro na Jahar Benue, sunyi nasarar cafke wani Matashi mai suna Odinaka Ugwuanyi mai kimanin shekaru 29, akan hanyar Apri dake Makurdi, dauke da Tramadol 124,000 da Diazepam da Exol-5, wanda suka kai nauyin kilograms 22.55.
Matashin anyi nasarar cafke shine da misalin karfe takwas na ranar Asabar cikin wata motar haya, yace ya fito ne daga Karamar hukumar Nsukka dake Jahar Enugu.
Matashin dai ya karyata kayan da cewa ba nashi bane ne, inda yace wani fasinja ne ya ajiye su ya ruga bayan ya hango jami’an NDLEA,.
Shugaban hukumar ta NDLEA Brig. Jan. Mohamed Buba Marwa (Retd) ya yabawa jami’an kan irin gagarumar nasara da suka samu wajan dakile safarar miyagun kwayoyi a Jahar ta Benue da jahar Enugu.
Brig. Gen. Mohamed Buba Marwa (Retd) ya kara basu himma kan jajircewa don hana safarar haramtattun kayayyaki a yankin baki daya.