Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta gargadi Maniyyata aikin hajjin bana kan su guji ta’ammali da miyagun kwayoyi.
Jami’ar hukumar Habiba Zubair ce ta bukaci hakan yayin da take jawabi ga Maniyyatan a Ilorin, lokacin da suke kokarin tashi zuwa Saudiyya.
Ta kuma shawarci Maniyyatan kan su dauki iya maganin da suka san cewa likita ne ya basu umarnin sha, wanda kuma bai sabawa da ka’idar gwamnatocin kasashen biyu ba.
Habiba ta kuma shawarci Maniyyatan kan gujewa guzurin goro zuwa Saudiyya, koda kuwa domin amfanin kan su ne, saboda hukumar Saudiyya ta hana ta’ammali da goron baki daya.
Daga nan sai ta shawarce su kan sanya tufafin da aka basu, da nufin sauƙin gane su a kasa mai tsarki, da nufin basu dukkan taimakon da ya kamata.
Ibadar aikin hajji dai ta kasance guda cikin shika shikan addinin musulunci, kuma tana wajaba ne akan wanda ya ke da hali a ƙalla sau daya a rayuwar sa.