Hukumar dakile safarar miyagun kwayoyi ta kasa, NDLEA a Kano, ta ce ta yi nasarar cafke wani mutum mai suna Ekennah Okechuku bisa zarginsa da safarar wiwi da nauyinta ya kai kilogiram 130.
Kwamandan NDLEA a Kano, Dr. Ibrahim Abdu ne ya shaidawa manema labarai hakan a ranar Alhamis a Kano. Inda ya kara da cewa hukumar su ta NDLEA ne ta kama shi ba wai hukumar KAROTA ba kamar yadda aka fara labarto wa ba.
“jami’anmu daga Abuja a titin Suleja, sune suka yi nasarar dakile safarar wiwi da ta kai kilogiram 50 a motar haya mallakin wanda ake zargi a hanyarsa ta zuwa Kano”. Ya tabbatar.
Kwamandan NDLEA din ya tabbatar da cewa mafi yawan masu wadannan kwayoyi ba su biyo kayansu ta motar da suka bayar, amma da suka shaida mana, mun yi bincike mun cafko kuma wanda ake zargi, inji shi.
Ya ce a yayin bincike ne suka sake gano wata wiwi din da nauyinta ya kai kilogiram 50 da wata da ta kai 35 mallakinshi da wata kamfanin zirga-zirgada take aiki a Ibadan.
“tunda wanda ake zargi yana hannunmu, dukkanin kwayoyi za a kawo su zuwa Kano, domin gurfanar da shi a gaban kotu bisa zargi guda uku”. Ya tabbatar.
Ya tabbatar da cewa suna da alaka da irin wadannan motoci, inda suka labarta musu a duk lokacin da suka ga wata alama wani na dauke da irin wadannan kwayoyi ko dai a hanyar zuwansa Kano ko zai bar Kano; “suna sanar damu”.
Tunda da farko dai, Babban Darakta KAROTA, Baffa Dan’agundi ya ce hukumarsa ce ta cafke shi, amma yanzu sun gyarota da NDLEA bisa sabanin da suka samu.
Ya nemi KAROTA da sauran hukumomi su ci gaba da ba su hadin kai, domin ganin sun yi nasarar dakile safarar kwayoyi a jihar.