Hukumar hana sha da fataucin muggan kwayoyi ta kasa NDLEA a yau Litinin ta gurfanar da wani mutum mai shekaru 28, Akanni Olapade a gaban wata Babbar Kotun Tarayya da ke Legas, bisa zargin sa da laifin “Ta’ammali da muggan kwayoyi”.
An tuhumi wanda ake ake zargi kan laifi guda daya; na safarar miyagun kwayoyi a cikin takaddar karar da aka shigar gaban Kotun Mai lamba; FHC/L/239c/2021.
Mai gabatar da kara, Mista Jeremiah Aernan ya yi zargin cewa, wanda ake kara ya aikata laifin ne a jiya Lahadi 26 ga watan Satumba shekarar 2021.
Ya Kuma yi zargin cewa, an cafke wanda ake kara ne garin Bolar Moke-Afa da ke yankin Isolo na jihar Legas, saboda kamashi da Tabar Wiwi mai nauyin gram 800.
KARANTA WANNAN LABARIN: Jami’an yan sanda sun kama Yan fashi da makami 8 a Nasarawa
A cewar mai gabatar da karan, Tabar Wiwi na daya daga ciki haramtattun kwayoyi kamar su Hodar Iblis, Heroine da dai sauran su.
Kazalika ya Kara da cewa, Laifin safarar miyagun kwayoyi ya ci karo da sashin na 11 (c) na dokar hukumar NDLEA, da kuma na dokar Gwamnatin Tarayya.
Wanda dokokin suka tanadi hukuncin daurin rai da rai idan aka sami Wanda ake zargi da aikata laifin.
Sai dai har kawo hada wannan rahoto, ba a tsayar da ranar da za a gurfanar da wanda ake tuhumar ba, a gaban Kotun.
A wani labarin Kuma na daban.
Akalla mutane biyu ne suka rasa rayukan su a jiya Lahadi, sanadiyar taho mugama da wani Dan OKada yayi da wata Mota a garin Akure babban Birnin jihar Ondo.
Hadarin ya afku ne kan hanyar wata sananniyar Asibiti dake yankin.
Fasinjoji buyu dake kan mashin Nan take suka mutu , yayin da wata Mota ta yi awon gaba da su ta baya,
Sai dai Matukin mashin din, Wanda shine na uku akan mashin din, ya tsallake rijiya da baya, bayan ya Sami mummunan raunika a jikin shi.
Kazalika hadarin yayi sanadiyar kawo tsunkoson ababen hawa a yankin, har natsawon wasu sa’o’i masu yawa
Sai dai wani shaidan gani da Ido ya bayyana wa majiyar Jaridar Dimokuradiyya cewa, hadarin ya na da alaka da gudun wuce kima da Direban Mota keyi.
Comments 1