NDLEA ta kama Baron na Ƙwaya 10, da masu laifi 17,647 a cikin watanni 17
Kimanin mutane dubu 17, 647 masu laifi da Baron na Ƙwaya aka kama a cikin watanni 17 da suka gabata, gami da yankewa mutane dubu 2,369 hukunci da ɗaure su, a yayinda mutane dubu 11,000 masu shan ƙwaya aka canja masu ɗabi’u, tare da yi masu magani a wannan lokacin.
Shugaban Hukumar na Ƙasa Birgediya-Janar Mohammed Buba Marwa mai ritaya ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi ga Manema labaru a ranar Litinin a Abuja.
KARANTA WANNAN LABARIN: 2023: Sultan, Tambuwal Sun yi kira ga Maniyyata Aikin Hajji dasu yi addu’ar samun Shuwagabanni Nagari
Mai Magana da Yawun Hukumar Hana sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Femi Babafemi a cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Litinin, yace wannan fara bikin ranar ƙwaya ta duniya ta Majalisar Dinkin Duniya ta tana da taken “Magance Matsalar Ƙwaya ga Lafiya,.
Sanarwar ta naƙalto Buba Marwa na cewa “gare mu a hukumar mu, muna sane da lokaci na gudunmuwar da muke bayar wa na magance Ƙwaya. A Shekarar 2021, kimanin mutane masu amfani da ƙwaya dubu 8,000 aka canjawa Aƙida, tare da yi masu magani, kuma mun cigaba da haka, inda a cikin watanni biyar na Shekara 2022, mun yi mutane dubu 3, 523 magani a cibiyoyin NDLEA.
“Mun cigaba da kama masu amfani da kwayu,inda muka kama mutane 17,647 mashaya, ciki har da baron na kwaya a tsakanin watan Janairun shekara 2021 da Mayu na shekarar 2022,.
“Mutane sama da dubu 2,369 an yanke masu hukunci, an kama Ƙwaya mai nauyin kilogaram dubu 154,667.339 a cikin farkon watanni biyar na wannan shekarar kaɗai.”
Comments 1