Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ta ce ta kama hodar Ibilis ta biliyoyin naira a ofishin ta ke a filin jirgin saman Murtala Muhammed na jihar Legas,
Ta kama kama wasu mutum uku ne da suka ƙudurta fataucin hodar Ibilis ɗin mai nauyin giram 137.8 zuwa Indiya.
Wakilinmu na Legas Umar Shehu Elleman ya tambayi shugaban hukumar NDLEA Garba Ahmadu da ke filin jiragen sama na Murtala Muhammad a Legas yadda kamen ya kasance.
Ku latsa lasifikar da ke ƙasa don sauraron hirarsu: